🌍 04/02/2026 – RANAR CANCER TA DUNIYA
“Mu waye, mu kare kanmu, mu ceci rayuka.
Cancer ba cuta guda ɗaya ba ce, cututtuka ne masu yawa da ke faruwa idan ƙwayoyin jiki suka fara girma ba tare da tsari ba. A yau muna tunatar da kowa
—musamman mata
muhimmancin sani, kariya, da gwaji da wuri
⚠️ ALAMOMIN CANCER
(Gabaɗaya)
Kiba ko raguwa ba tare da dalili ba
Gajiya mai tsanani kullum
Ciwon da baya warkewa
Jini ko ruwa daga jiki ba daidai ba
Canjin fata ko kumburi
Tari mai ɗaukar lokaci ko wahalar numfashi
👩🦰 ALAMOMI MUSAMMAN GA MATA
Kumburi ko ciwo a nono
Jini daga farji ba lokacin al’ada ba
Ciwon mara ko ƙasan ciki mai ɗorewa
Canjin siffa ko launin nono
Zafi yayin saduwa
DABI’U DA KE HADDASA CANCER
Shan taba sigari ko shakar hayakinta
Shan barasa
Cin abinci mara kyau (mai yawan mai, gishiri, da sukari)
Rashin motsa jiki
Gurɓataccen muhalli
Kamuwa da wasu ƙwayoyin cuta (misali HPV, Hepatitis)
Yawan fuskantar hasken rana ba kariya
🛡️ HANYOYIN KARIYA
(MUSAMMAN GA MATA)
Yin gwajin nono da gwajin mahaifa (Pap smear) akai-akai
Kar a sha taba ko barasa
Cin abinci mai gina jiki (’ya’yan itatuwa, kayan lambu)
Yin motsa jiki akai-akai
Yin allurar rigakafi (HPV, Hepatitis B)
Zuwa asibiti da wuri idan an ga canji
Rage kiba, kula da lafiyar jiki
💬 SAKO NA KARSHE
Gano cancer da wuri = rayuwa.
Mu wayar da kanmu, mu fadakar da ’yan’uwa, mu kare mata da al’umma
baki ɗaya.
Allah shine masani
Dan tambayoyi Ko Karin bayani jeki shafin Lafiyar mace 👇
https://www.facebook.com/profile.php?id=61580665618700
✍️ Lafiyar mace
#WorldCancerDay #CancerAwareness #LafiyarMace #PreventionIsBetterThanCure