Imam Hussaini (A.S) ya kama hanyar zuwa Karbala a ranar 8 ga watan Zul-Hijja, shekara ta 60 bayan Hijira, wato a ranar da ake kira Yawm at-Tarwiyah — rana guda kafin Arafah (9 ga Zul-Hijja).
A wannan rana, Imam Hussaini (A.S) ya fice daga Makka ba tare da kammala aikin Hajji ba, ya koma Umrah saboda hadarin da yake fuskanta daga sojojin Yazid da aka tura don su kashe shi har a cikin harami. Sai ya nufi kasar Iraq ne da iyalinsa da magoya bayansa bayan ya samu wasiku daga mutanen Kufa suna kiran ya zo su yi masa mubaya’a.
Zuwan Imam Hussaini (A.S) zuwa Karbala ya kai shi can ranar 2 ga watan Muharram, inda daga nan aka dasa sansani har zuwa ranar Ashura – 10 ga Muharram, lokacin da aka yi masa shahada.
Ya Hussain Labbaika Ya Mahadii ��
Stay in the loop for updates and never miss a thing. Are you interested?
Yes
No
Undo
Interested
Ticket Info
To stay informed about ticket information or to know if tickets are not required, click the 'Notify me' button below.