*_Ya fada masa sirrin dake tsakaninsa da Allah wadda bai fadiwa kowaba.!_*
_"Shaheed Ahmad Agha"_
*_Dr. Mohsen Nouri yake cewa, "an iya bada tabbaci cewa Ahmad Agha ba shi da wani buqata ta "kai" Ba shi da wani girman buqata ta qashin kai nashi da zai zama shamaki tsakaninsa da Masoyinsa (Allah). Wataƙila wannan na daga dalilai da alamar da ya sa ya sami wasu sirrika na gaibiyyah masu girman gaske._*
_Wasu lokutan yakan yi mana magana game da wasu batutuwa don amfaninmu da kuma tsari don maslaharmu. Ya kasance yana yin hasashen abinda zai faru nan gaba, waɗanda suke da kima a gare mu._
*_Ni abokin Ahmad Agha ne. Na tuna wata rana a cikin ’yan shekarun nan, ya ce mini wani abu mai ban mamaki a wani wuri. Ina da wani sirri tsakanina da Allah wanda ba wanda ya sani.
Ahmad Agha ya ce da ni cikin hikima, “Kana da buri biyu, kuma ka roki wadannan burikan biyu a wajen Allah, ko Allah ya ba ka su!? Ya dogara ne idan ka kula da motsinka da ayyukanka da kuma tsarkake ruhi har zuwa ranar Ashura”. Na yi matukar kaduwa._*
_Ya ba ni shawarar cewa: “Idan kana son yin taka tsantsan ne, to ka kiyaye ayyukanka daga yanzu kafin Ashura har zuwa ranar Ashura, kuma ka kiyaye kada ka yi sakaci. Ya ci gaba da cewa, “Allah zai cika daya daga cikin wadannan bukatu naka a wannan Ashura matukar dai ka yi taka tsantsan."_
*_Alhamdulillahi a wannan shekarar ina cikin yanayi mai kyau. Na yi ƙoƙari sosai don kada in yi wani zunubi. Sannan har watan Muharram tazo. A cikin kwanaki goma na farkon watan, na ƙara kiyayewa da tsantseni kwarai don kada inyi wani kuskure._*
_Bayan kwanaki biyu zuwa uku, sai na ga Ahmad Agha a masallacin Amindoleh, sai mukai sallama ba musabaha, ya dan matse hannuna kamar yadda ya saba, ya ce, “Madallah da kokarinka! Kayi tsantsane yadda ya kamata kuma na taya ka murna._
*_Sa'annan ya ce mini, "Za ka so in gaya maka abin da ka roka a wajen Allah?" A bisa amana da soyayyar da na yi masa na ce, “A’a, ba sai ka fadi min ba ma. Bayan wadannan kwanaki biyun, burina na farko ya cika. Lokaci ya cigaba da tafiya har zuwa jajibirin Arbaeen. Ahmad Agha ya ce da ni, “Allah yana son ya biya maka buri na biyu, amma yana jiran ya ga ko zaka kula da ayyukanka zuwa ranar Arba'in." Don haka sai na sake yin taka tsantsan har zuwa ranar Arba'in, amma sai ya zama nayi wani kuskure.!_*
_Wani mutum ne ya fara "GIBA" (muna zaune ana fira), ni kuma a wannan yanayin ya zama wajibi in hane shi wannan mugunyar dabi'an a lokacin. Amma saboda taka tsantsan ban ce komai ba, na mike har na dan yi dariya. Nan da nan da sauri na gane kuskure na. Bayan nan, na cigaba da taka-tsan-tsan don tabbatar da cewa wani kuskure bai sake afkuwa ba cikin ayyukan a wannan lokacin. Haka na yi ta yi har washegarin bayan Arbaeen._
*_Bayan Arbaeen na tafi wajen Ahmad Agha. Na tambayi kaina daga gare shi, sai ya ce, "Abin takaici, yanayin bai yi kyau ba, Allah ba zai biya maka wannan buri ba a yanzu." Sa’an nan kuma ya fara magana kan taron gulma na (Giba) da na halarta, ya ce, “Baka iya yin taka tsantsan lokacin da ake bukata ba.!_*
_Wannan fahimtar da abokansa muka yi na tarbiyyar Ruhibsa ya sanya Ahmad Agha ya zama fiye da abokinmu, bawai abokin kawai ba, ya kasance Koci kuma malamin da'a a tsakaninmu. Mu da abokanmu muna matukar son Ahmad Agha._
*_Mun yi tarayya da shi da matuƙar So. Mu duka ni da sauran mutanen masallaci muna son shi. Sai dai Ahmad ya ci gaba sosai a wannan tafiya ta Ruhiyyah, ya ratsa manyan matakai masu girma da yawa har ya zama ya kusanci kusanci Hazratul Haq (Allah) kusanta sosai, har sai da ya zama abu mai wahala mauka a gare shi ya ci gaba da zama da rayuwa a wannan Duniyar tamu._*
_...Journalist Daddy_